Hukumar Kare Hakkin bil-adama zata yi bincike a Baga

Baga
Image caption Baga

Hukumar kare hakkin bil-adama ta Najeriya ta ce zata gudanar da bincike domin tantance abun da ya faru a garin Baga na karamar hukumar Kukuwa a jihar Borno.

Hukumar ta ce tuni yanzu ta soma tattara bayanai game da lamarin.

Ta kuma ce nan bada jimawa ba zata aike da wata tawaga zuwa garin don gane ma idanunta abun da ya faru a lokacin da jami'an tsaron kasar suka yi artabu da wasu 'yan bindiga da ake zargin cewa 'yan kungiyar nan ce da aka fi sani da Boko Haram ce.

Arangamar da aka yi dai ta janyo asarar rayuka masu yawa da kuma kona gidajen jama'a. Rundunar sojojin Nigeria ta ce mutane 37 ne suka rasa rayukansu, yayin da jama'a mazauna garin ke cewar an hallaka mutane sama da 200.