Durawa fursunonin Guantanamo abinci laifi ne

Fursunan Guantanamo
Image caption Fursunan Guantanamo

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tilastawa fursunonin dake yajin cin abinci a sasanin Guantanamo su ci abincin ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Hukumar tace idan ta tabbata cewa ana tilastawa mutane cin abinci ba da son ransu ba, to kuwa za ta dauki wannan mataki a matsayin keta da rashin imani.

Shugaban Amirka Barack Obama yace baya fatan ganin wani fursuna a sansanin na Guantanamo ya rasa ransa yana mai cewa zai sabunta yunkurin ganin an rufe sansanin.

" Ya ce, sansanin Guantanamo bai zama wajibi ba domin tsaron lafiyar Amirka. Hasali ma yana da tsada kula da sansanin sannan kuma yana zubar da martabar Amirka a idanun duniya."

Karin bayani