Kotu ta ce tsare Tymoshenko ya saba ka'ida

Yulia Tymoshenko
Image caption Yulia Tymoshenko

Kotun kare hakkin dan Adam ta hukumar tarayyar turai ta zartar da hukuncin cewa alkalai a Ukrain sun yi kuskure a umarnin da suka bayar na tsare tsohuwar Firayi ministar kasar Yulia Tymoshenko.

An dai tsare tsohuwar Firayi ministar a gidan yari ne a lokacin da ake yi mata shari'a kusan shekaru biyu da suka wuce.

Kotun ta Strasburg ta ce tsarewar da aka yi mata an yi ta ne bisa son zuciya ba bisa ka'idojin da suka dace da shari'a ba.

Sai dai kuma Kotun ta yi watsi da zargin da Mrs Tymoshenko ta yi cewa an ci zarafinta a lokacin da ake tsare da ita.