Najeriya: An mika rahoton farko kan rikicin Baga

Garin Baga a arewacin Jihar Borno, Najeriya
Image caption Garin Baga a arewacin Jihar Borno, Najeriya

Helkwatar tsaron Najeriya da Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA, sun mika rahoton farko ga shugaban kasar game da binciken hare-haren da suka abku a garin Baga.

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a rikicin na Baga dake arewacin jihar Borno.

An dai yi ta samun rudani game da adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari.

Rahoton ya ce a ranar 17 ga watan na Afrilu dakarun rundunar tsaron ta hadin guiwa sun gudanar da aikin bincike a wurin da akayi artabun inda suka gano wasu kayayyaki da 'yan kungiyar Boko Haram suka gudu suka bari.

Kayayyakin sun hada da bundugogin harba makaman roka da samfurin AK 47 da harsasai iri dabam daban da bama bamai hadin gida iri dabam daban, da kuma wata mota kirar jeep da aka lalata.

Rahoton ya kara da cewa ba kamar yadda aka yi zargin cewa mutane 185 sojojin rundunar tabbatar da tsaron ta hadin guiwa sun kashe a garin na Baga ba,yace bincike ya nuna cewa 'yan ta'adda 30 aka kashe a bata kashin.

An kuma gano gawarwaki shida a tafkin chadi da ke tazarar kilomita uku daga wurin da aka yi artabun.

Rahoton ya ce bayanan da aka samu daga wasu mazauna garin game da ko za su iya nunawa ayarin masu binciken inda kaburbran mutane 185 din aka ce sojojin sun kashe suke, mutanen sun ce basu masaniya.

Tuni dai hukumar kare hakkin bil'dama a Najeriya ta ce ta soma tattara bayanai game da lamarin.

Hukumar ta ce nan bada jimawa bane zata aike da wata tawaga domin gudanar da bincike kan zargin da wasu keyi cewa jami'an tsaron kasar sun yi amfani da karfi fiye da kima, a artabun da suka yi da wasu 'yan bindiga, da ake zargin cewa 'yan kungiyar nan ce da aka fi sani da Boko Haram.