Bayern Munich ta yi waje da Barcelona

Kulob din Bayern Munich ya yi waje da Barcelona ta hanyar caccasa su da ci 3-0 a filin wasa na Nou Camp.

Hakan dai ya sa kulob din ya kafa tarihi a yawan kwallayen da ya ci a wasan kusa da na karshe a gasar ta cin kofin zakarun turai da kwallaye 7-0.

Arjen Robben ne ya fara jefa kwallo a ragar Barcelona jim kadan bayan hutun rabin lokaci.

Gerard Pique na Barcelona ne ya yi kukuren cin kansu da kansu da kwallo ta biyu yayin da Thomas Muller shi ma ya fasa ragar Barcelona da kwallo ta uku.

Kulob din na Bayern a yanzu zai hadu ne da takwaransa na kasar Jamus Borussia Dortmund a wasan karshe da za a buga ranar 25 ga watan Mayu a filin wasa na Wembley da ke birnin Landan.