Hukuncin: na'urar gano bam na bogi

Image caption Na'urar gano bam na bogi

A yau ne za'a bayyana hukuncin da aka yankewa wani hamshakin dan kasuwa a Burtaniya bayan ya siyarda wasu na'urorin gano bam na bogi.

Ana dai kyautata zaton hamshakin dan kasuwan James McCormick ya samu ribar dalan amurka miliyan takwas bayan ya siyarda na'urorin.

Har wa yau ya shaidawa wadanda ya siyarwa na'urorin cewa, na'urar zata iya gano mutanen dake dauke da miyagun kwayoyi baya ga bama-bamai.

Gwamnatin kasar Nijar dai ta kashe sama da dalan Amurka dubu dari biyu inda ta sayi na'urori goma a shekara ta 2008 bayan dan danfaran ya yiwa jami'an kasar gwajin bogi.

Jami'an yansanda a Burtaniya sunce anyi aiki da na'urar a shingayen duba ababen hawa, inda anan ne aka gano cewa na'urar bata aiki.

Gwamnatin Nijar dai ta bukaci dan kasuwar da ya mayar mata da kudin ta bayan da wasu bama-bamai suka tashi a babban birnin kasar Yamai.

Dan kasuwan dai yaki biyan kudin kuma gwamnatin Niger dai bata kai batun gaba ba.

Kamfanin dan kasuwan wato ATSC ya siyarda na'urorin a kasashen Afrika da kuma kuma gabas ta tsakiya da dama.

A makon da ya gabata ne da wata kotu a Burtaniya ta samu dan kasuwan da laifin damfara.