Kungiyoyin kwadago a kasar Girka zasu shiga yajin aiki

Yajin aiki da zanga-zanga a kasar Girka
Image caption Yajin aiki da zanga-zanga a kasar Girka

Kungiyoyin kwadago a kasar Girka zasu gudanar da wani yajin aikin gama gari don bikin ranar ma'aikata ta duniya.

An dai shirya gudanar da zanga-zanga a sassa dabam dabam na kasar inda jami'an 'yan sanda suka kasance cikin shirin ko ta kwana.

Masu zanga zangar dai na kira ne da aka kawo karshen shirin tsuke bakin aljihu na gwamnati, wanda yayi sanadiyar karuwar rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa.

Kasar Girka ta shafe kusan shekaru shida kenan tana fama da matsalar koma bayan tattalin arziki.

Sai dai gwamnati ta ce daukar irin wadannan matakan ya zama wajibi don samun karin tallafi kudade daga kasashen waje.