Yara na cikin mummunan hali a Iraqi- In ji War Child

Wasu yara a Iraqi
Image caption Wasu yara a Iraqi

Kungiyar agaji ta War Child ta bayyana halin da yara kanana ke ciki a Iraqi da cewa yana daya daga cikin wadanda aka fi yin watsi da su a rikice-rikicen da suka faru a duniya.

Kungiyar ta soki kasashen da suka shiga cikin yakin da yin watsi da rayuwar yaran bayan bayyana kawo karshen yakin, yau shekaru goma da suka wuce.

Kungiyar ta kara da cewa ya zuwa yanzu a wannan shekarar, kananan yara da kuma matasa 'yan kasa da shekaru 25 fiye da 700 ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan da suka faru a kasar ta Iraqi.

Sannan kuma kungiyar ta War Child ta ce daya daga cikin yara hudu na fama da tamowa sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

Karin bayani