Jose Mourinho na iya komawa Ingila

Image caption Jose Mourinho zai iya barin Real Madrid

Mai bada horo na Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Jose Mourinho ya ce ba lalle ne ya ci gaba da zama mai bada horo na kulob din ba a kakar wasanni mai zuwa.

Mourinho, ya ce ya na shirin komawa inda a ke son sa.

" 'Yan kallo na sona haka ma kafafan yada labarai na yi min adalci," inji Jose Mourinho, tsohon mai bada horo na kulob din Chelsea.

Dan kasar Portugal mai shekaru 50 an danganta shi da yunkurin fita daga Spain; kuma ya taba magana a baya ta komawarsa Ingila.

Karin bayani