Dan marigayi Gaddafi zai bayyana a Kotu

Image caption An dai kama Saif Al Islam ne a garin Zintan

A yau dan marigayi Kanal Gaddafi wanda ake tsare da shi a garin Zintan dake Libya zai bayyana a Kotu.

Ana dai tuhumarsa ne da da aikata manyan laifuka.

Kotun hukunta mayan laifuka ta duniya itama na son ta gurfanar da shi game da zargin aikata laifin yaki a shekara ta 2011.

Sai da gwamnatin Libya na kokarin gurfanar da shi ne a kasarsa ta haihuwa.

Sayef Al-Islam Gaddafi zai bayyana ne a wata kotun hukuntan manyan laifuka dake Zitan a karo na biyu a bana.

Yana fuskantar tuhuma ne akan musayar wasu bayanan sirri da mallakar wasu takardu dake da illa ga tsaron kasa da kuma cin mutunci tutar kasa.

A fara shari'ar ce a watan Junairun da ta gabata amma aka daga shari'ar saboda babu lauyan dake wakiltarsa.

Tun daga wannan lokaci dai babu alamun cewa akwai lauyan da zai wakilce shi.

Har wa yau a alankanta tuhumar da ake masa ga wata lauyar kotun hukunta manya laifuka ta duniya wato Melinda Taylor da kuma wani abun abokin aikinta.

An dai tsare su ne na kusan wata guda a Libyan bayan sun kai masa ziyara a watan Yunin bara.

An zargi lauyoyin da mika mishi wasu wasiku daga wani na hannu damarsa da kuma taya shi leken asiri.

Daga baya dai an sake su inda aka mikasu birnin Hague.

Za'ayi shari'ar Melinda Taylor ne da kuma abokin aikinta duk da cewa basa Libya a yanzu haka.