Kotun Kenya ta samu wasu Iraniyawa da kulla makarkashiya

Wasu Iraniyawa
Image caption Wasu Iraniyawa

Wata Kotu a Kenya ta samu wasu 'yan kasar Iran da laifin shirya makarkashiyar kai hare haren ta'addanci a kan wuraren Isra'ila da Amurka da kuma Birtaniya dake a kasar.

Mutanen -- Ahmed Abolfathi Mohammed da kuma Sayed Mansour Mousavi -- an kuma same su da laifin mallakar wani katon bam mai nauyin kilo 15.

Masu gabatar da kara sun shedawa kotu cewar mutanen -- wadanda suka musanta tuhumar -- zaratan sojin Iran ne -- wato Revolutionary Guards.

A ranar Litinin ne za a bayyana hukuncin da za a yanke masu.

Alkalin kotun majistaren ya ce matakin da 'yan sandan Kenya suka dauka ciin hanzari wajen kama mutanen, shi ya hana aikata barna, da asarar rayuka masu dimbin yawa.