Fari ya 'kashe mutane 260,000 a Somalia'

Image caption Dubun dubatar mutane ne suka kauracewa gidajensu domin neman abinci.

Kimanin mutane 260,000 ne suka mutu sakamakon farin da ya afkawa kasar Somalia daga shekara ta 2010 zuwa 2012, kamar yadda bincike ya nuna.

Kusan rabinsu yara ne 'yan kasa da shekaru biyar, a cewar rahoton Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu gargadi kan fari na Amurka.

Adadin wadanda suka mutun ya zarta 220,000 da aka yi kiyasin sun mutu a lokacin farin da aka yi fama da shi a 1992.

Lamarin ya yi kamari ne sakamakon karancin ruwan sama, da tsanantar fada tsakanin kungiyoyin da ke fada da juna.

Wani babban jami'i na Hukumar samar da abinci ta FAO Mark Smulders ya ce "ainahin illar da lamarin ya haifar ta fito fili sakamakon binciken da aka gudanar.

"Wannan ya nuna cewa abinda ya faru a Somalia na daya daga cikin fari mafi muni da ya afku a duniya cikin shekaru 25 da suka gabata," kamar yadda ya kara da cewa.

Somalia ta fuskanci matsalar fari a shekara ta 2011 bayan da yankin kusurwar Afrika ya fada cikin matsanancin bala'in fari da yunwa.

Dubun dubatar mutane ne suka kauracewa gidajensu domin neman abinci.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kawo karshen farin a watan Fabrerun shekara ta 2012.

Karin bayani