Amurka ta nemi Korea ta Arewa da ta sako dan kasarta

Mr Kenneth Bae
Image caption Mr Kenneth Bae

Gwamnatin Amurka ta bukaci Korea ta Arewa da ta gaggauta sakin wani BaAmurke da ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 15 tare da aikin wahala a gidan yari.

A cikin watan Nuwanba ne dai aka kama Kenneth Bae yayinda yake jagorantar wani gungun maziyarta a kasar.

Kafar watsa labaran Korea ta Arewa ta ce Mr Bae ya amsa tuhumar kokarin hambarar da gwamnatin kasar.

Wani Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Patrick Ventrell, ya ce gwamnatin Amurka na da dadaddiyar damuwa game da rashin nuna gaskiya a tsarin shari'ar Korea ta Arewa sannan ya nemi a yiwa Mr Bae ahuwa.

Karin bayani