Baga: Amurka na nazari kan zargin cin zarafin bil'adama

Barnar da aka yi a garin Baga
Image caption Barnar da aka yi a garin Baga

Ofishin jakadancin Amurka a Nigeria ya ce yana nazari kan zarge-zargen da ake yi na cewa sojojin Najeriya sun aikata laifukan take hakkin bil'adama a hare-haren da aka kai a garin Baga na jihar Borno.

Amurkan ta kuma ce a yanzu ta fito da wata hanya ta takaita bada takardar izinin shiga kasar ga wasu jami'ai a Najeriyar da ake zargi da yin sama da fadi da dukiyoin al'umma.

Jakadan Amurka a Najeriya ya bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da ya yi da kungiyoyin kare hakkin bil'adama, inda suka tabo batutuwa da dama da suka danganci cin hanci da rashawa.

An dai zargi rundunar sojin Najeriya da kisan fararen hula fiye da 200 a garin Baga na Maiduguri - zargin da ta musanta, tana mai cewa mutane 37 ne kawai suka mutu.

Jakadan na Amurka ya bayyana wa kungiyoyin cewa akwai wata dokar kasar ta Amurka da ta hana su bayar da tallafi ga duk wata rundunar sojin kasa da ke musguna wa fararen hula.

Ba mu kai ga janye tallafi ba tukunna

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wata sanarwa da ke musanta wasu rahotannin kafafen watsa labarai da ke cewa ta janye tallafin kayan sojan da take ba Najeriya, sakamakon tashin hankalin da ya faru a garin Baga na jihar Borno.

Sai dai ma'aikatar ta ce tana nazari a kan binciken da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right Watch ta yi game da rufa-rufar da ta ce gwamnatin Najeriyar na neman yi game da kisan gillar da ake zargin sojoji sun yi a garin na Baga.

Ma'aikatar harkokin wajen ta ce har yanzu Najeriya tana cikin kawayen Amurka na Afrika da take bawa tallafin horon soja da ake wa lakabi da ACOTA a takaice.

Sai dai sanarwar ta ce Amurka har yanzu ta dauki batun tabbatar da cewa kasashe ba sa keta hakkin bil adama da muhimmanci.

A don haka tana nazarin rahoton da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta fitar, da ke nuna cewa jami'an Najeriya na kokarin yin rufa-rufa a kan lamarin da ya faru a Baga.

Wasu mazauna garin na Baga ne suka zargi sojoji da kai wa fararen hula hare-hare da gangan.

Hakazalika ma'aikatar ta ce wani babban jami'in gwamnatin Amurka mai kula da hakkin bil adama zai ziyarci Najeria a makon gobe domin ganin halin da ake ciki.

Batun cin hanci da rashawa

Taron ya kuma tabo batun cin hanci da rashawa a Najeriya, inda kungiyoyin suka bukaci Amurka da ta taimaka wajen ceto talakawan Najeriya daga matsalar.

Kungiyoyin sun kuma bada misali da yafe wa tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamaseigha da gwamnatin Najeriya ta yi, a matsayin wata alama da ke nuna cewa gwamnatin kasar ba da gaske take ba a yakin da take ikirarin yi da almundahana a kasar.

Jakadan na Amurka ya ce, a duka lokacin da suka hadu da jami'an Najeriya suna taso musu da batutuwan.

Inda ya ce gwamnatin Najeriya ta bayyana rashin jin dadinta da sukar da Amurkan ta yi wa Najeriyar kan yafewa Alamaseigha.

Karin bayani