Jakadan Amurka a Najeriya ya gana da kungiyoyin kare Hakkin BilAdama

Barnar da aka yi a garin Baga
Image caption Barnar da aka yi a garin Baga

A yau ne kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka yi wata ganawa da jakadan kasar Amurka a Najeriya, inda suka tabo batutuwa da dama da suka danganci cin hanci da rashawa da ya yi katutu a Najeriya da kuma rashin hukunta wadanda ake zargi da aikata laifuka.

Kungiyoyin sun nemi Amurka da ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da matsalar cin hanci a kasar, kuma sun bada misalin yafewar da gwamnatin Najeriyar ta yiwa tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamieyesegha, a matsayin wata alama dake nuna cewa gwamnatin ba da gaske take ba a yakin da take ikirarin yi da almundahana a kasar.

Jakadan na Amurka, Mr Terence McCulley ya bayyana wa kungiyoyin cewa akwai kwararan shaidu da suka nuna cewa sojojin Najeriya suna keta Hakkin fararen hula,kuma akwai wata dokar kasar ta Amurka da ta hana su bayar da tallafi ga duk wata rundunar sojin kasa da ke musguna wa fararen hula.

Hakazalika, jakadan na Amurka ya ce Amurka ta bullo da wata sabuwar hanya inda za ta taikata bada takardar izinin visa na shiga Amurka ga duk wasu jami'an gwamnatin Najeriya da ake zargi da yin sama da fadi da dukiyar jama'a.

Karin bayani