An sallami alkali a Kano bisa cinye dukiyar marayu

Hukumar Kula da dauka da kuma ladabtar da ma'aikatan sharia ta Kano, wato Judicial Service Commission ta kori wani alkali a jihar bisa samun sa da laifin cinye dukiyar marayu.

Hukumar dai ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan korafe -korafe da ta samu akan alkalin daga wasu da shari'a ta kai su gaban sa.

Alkalin dai na aiki ne a kotun muslunci a Kano.

Jami'in hulda da jama'a na babbar Kotun jihar Kano, Baba Muhammed Jibo ya shaidawa BBC cewa Hukumar ladabtarwan ta samu alkalin da laifin salwantar da dukiyan marayu da shi da rajistaran kotun.

Tuni dai Hukumar ta sallami rajistaran daga aiki.

An dai jima dai ana zargin ma'aikatan shari'a da karbar cin hanci da rashawa da kuma danne hakkin mai karamin karfi a yayinda kuma kudi ke tasiri a lokacin yanke hukunci.

Ko a watan jiya ma, babbar mai shari'ar Najeriya, Justice Maryam Mukhtar ta dakatar da wani babban alkalin kotu dake Abuja bayan an same shi da laifin saba dokar aiki.

Karin bayani