'Yan bindiga sun sace Shettima Ali Monguno

Image caption Taswirar Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun sace daya daga cikin dattawan jihar Borno da ma arewacin Najeriya Dr Shettima Ali Monguno, jim kadan da fitowarsa daga sallar juma'a a garin Maiduguri.

Wasu 'yan bindiga ne dai suka aukawa motar da Shettima Ali Monguno yake ciki kana suka fitar da shi

Dokta Shettima Ali Monguno ya yi minista a jamhuriya ta farko, kuma yana cikin dattijan arewa.

Jihar Borno dai na fama da tashin hankali dake da nasaba da kungiyar da ake kira Boko Haram.

Dr Monguno yana cikin dattawan da suka gana da shugaban Nigeria Goodluck Jonathan kan yadda za a shawo kan rikicin Boko Haram a Maiduguri a watan Maris.

Ya dade yana kiran da a tattauna da 'ya'yan kungiyar sannan ya nemi shugaba Jonathan ya rage yawan dakarun sojin da aka tura yankin.

Tashe-tashen hankula masu alaka da Boko Haram sun haifar da asarar dubban rayuka tun daga shekara ta 2009.