An harbe mai binciken Kisan Benazir Bhutto

Chaudry Zulfiqar Ali
Image caption Chaudry Zulfiqar Ali

'Yan bindiga a Islamabad babban birnin Pakistan sun kashe mai gabatar da kara na musamman dake binciken kisan tsohuwar Pirayim Minista, Benazir Bhutto.

Wasu mutane ne a kan babura suka harbe Chaudhry Zulfiqar Ali yayinda yake tafiya a mota zuwa kotu, ya kuma mutu a asibiti daga bisani.

Kakakin asibitin da aka kai Chaudry Zulfiqar Ali, Waseem Khwaja ya ce an yi masa harbi ne a wurare fiye da 7 da harsasai suka huda, galibinsu ta gaba da kuma gefe.

Ya ce daya daga cikin harsashen ya bi ta kai,ya huda kokon kansa, haka kuma an karya gabar hannun dama da kuma hannun hagun.

Chaudry Zulfiqar Ali, shi ne babban mai gabatar da kara a wata shara'ar da take da nasaba da harin da 'yan gwagwarmaya suka kai a birnin Mumbai na India a 2008 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 166.

Tsohuwar Fira Minista Bhutto ta rasu ne a lokacin wani harin bindiga da na bam a wani gangamin yakin neman zabe da take gudanarwa a shekara ta 2007.

Hukumomi a Pakistan dai sun zargi kungiyar Taliban da hannu a kisan na tsohuwar Fira Ministar da aka yi a birnin Rawalpindi.

An dai zargi jami'an gwamnati da dama da hannu a kisan nata daga ciki ma har da tsohon shugaban kasar Pervez Musharraf, inda aka yi zargin cewa ba'a bata cikakken tsaro ba a lokacin da ta dawo kasar bayan gudun hijirar da ta yi.

Mr Musharraf dai ya yi watsi da zargin da ake masa inda yace akwai manufar siyasa a ciki.

Karin bayani