Amurka za ta dauki mataki a kan Syria- Obama

Image caption Mista Obama ya ce Amurka za ta yi duk mai yiwuwa domin kawo karshe rikicin Syria

Shugaba Obama ya ce Amurka tana duba duk hanyoyin da taga ya dace domin ganin ta kawo karshen yakin basasan da ake yi a kasar Syria.

Kalamun nasa sun zo ne bayan da sakataren harkokin tsaron kasar Amurka wato Chuck Hagel ya ce kasar na duba yiwuwar mikawa 'yan tawatan Syria makamai.

Kalaman shugaban na Amurka da na sakataren harkokin tsaron kasar na nuna cewa kasar na taka tsan-tsan da batun na mikawa 'yan tawayen makamai.

Dukanninsu biyu dai sunce ya zuwa yanzu ba'a yanke hunkunci ba game da wannan batu.

Amma hakan dai na nuna cewa Amurka ta fara sauya matsaya game da yakin na Syria.

An kiyasta cewa dai yakin na Syria ya yi sanadiyar asarar rayuka dubu saba'in.

A watan da ya gabata, fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce ta samu bayyanan sirri da ke nuni da cewa akwai yiwuwar gwamnati Assad ta yi amfani da makamai masu guba a yakin da take yi da'yan tawaye.

Shugaba Obama dai a baya ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yiwa gwamnatin kasar cewa ta mika 'yan tawaye makamai.

Amurkan dai ta ce bazata tura dakarunta kasar ba, amma ganin cewa Burtaniya ta tsoma bakinta a lamarin akwai yunkuri da Amurka ke yi domin ganin cewa ita ta sa hannu a yankin da ake yi a Syria.