CAR: Za'a bincika keta haƙƙin bil'adama

Image caption Tsohon shugaba Bozize, wanda za'a binciki mulkinsa

Gwamnatin wucin-gadi ta jamhuriyar Afurka ta tsakiya tace, ta soma binciken keta haƙƙin bil'adama da aka aikata a lokacin mulkin Francois Bozize.

Cikin watan Maris ne dai gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye ta Seleka suka tumbuke Francois Bozize daga kan karagar mulki.

Gwamnatin wucin-gadin dai tayi alkawarin gudanar da zabe cikin watanni goma sha takwas.

Sabon ministan shari'a na kasar yace, keta hakkin bil'adama da za'a bincika sun hada da aikata kisa, tsarewa babu hujja, da kuma azabtarwa da kuma sace mutane ayi garkuwa da su.