Jami'an tsaro sun kashe masu zanga-zanga a Guinea

A kalla an kashe mutane uku a Guinea a yayin wata gwabzawa tsakanin jami'an 'yan sanda da masu zanga-zangar da ke kira da a gudanar da sahihin zabe.

Wani babban jami'i jam'iyyar adawa ya ce wadanda aka kashen magoya bayan jam'iyyar adawa ne.

Masu adawa a kasar ta guinea sun ce shugaba Alpha Conde bai tuntube su ba kafin ya sanar da ranar da za a gudanar da zaben yan majalisu wato talatin ga watan yuni ba.

Karin bayani