Isra'ila ta kai hari cikin Syria

Jami'ai a Amurka sun ce Isra'ila ta kai hari cikin Syria tsakanin ranar alhamis zuwa Juma'a.

Labaran dake fitowa na cewa Isra'ila ta kai hari cikin Syria na da sarkakiya ganin cewa fadar gwamnatin Amurka ta White taki ta ce uffan game da batun a yayinda jami'an Isra'ila suka ki bada tabbacin cewa sun kai harin.

Amma wasu jami'ai a gwamnatin Amurka wadanda suka ki a bayyana su sunce Isra'ila ta kai harin daga daren ranar alhamis zuwa juma'a kuma akwai yiwuwar cewa an kai harin ne a inda ake tara makamai a kasar.

Jiragen yakin Isra'ila dai basu wuce ta saman Syria ba, sun kaddamar da harin ne daga sarrarin samaniyar Lebanon. Jiragen yakin Isra'ilan dai na yawan shawagi a sararin samaniyar Lebanon a kusan ko da yaushe amma a daren ranar alhamis yawan jiragen sun karo a yayinda suke atisayen kaddamar da hari.

Jakadan Syria a Majalisar dinkin duniya ya ce bashi da masaniya ko Isra'ila ta kai harin a cikin kasarsa amma a farkon wannan makon Ministan tsaron Isra'ila ya amince cewa kasarsa ta taba kai hari a cikin Syria a watan Junairun da ta gabata.