Portugal ta sanar da sabbin matakan tsuke bakin aljihu

Firaministan Portugal Pedro Passos Coelho ya sanar da sababbin matakan tsuke bakin aljihu domin kaucewa tallafin kasashen duniya.

A wani sakon sa ta kafar talbijin, ya ce shekarun ritaya daga aiki zasu fara ne daga sittin da biyar zuwa da shida daga yanzu.

Ya kuma sanar da shirin rage wasu ayyuka a gwamnati guda dubu talatin, inda ya kara da cewa, yanzu za a bukaci ma'aikatan gwamnati da su rinka kara sa'a guda akan sa'oin aikin su, wanda hakan zai kawo cewa suna aikin sa'oi arba'in a mako guda.

Ya ce yin hakan zai taimaka wajen adana fiye da dala biliyan shida a shekaru uku.