Ana zargin kisan kiyashi a Syria

Kisan Kiyashi a Syria
Image caption Kisan Kiyashi a Syria

Masu fafutuka a Syria sun bayyana cewa dakarun gwamnati sun kashe mutane da dama a wani abu da suka kwatanta a matsayin kisan kiyashi a kusa da garin Albanias, yankin dake gabar ruwa a arewa maso yammacin kasar.

Masu fafutuka sun ce suna da bayanan dake cewa an kashe akalla mutane 77 a unguwannin 'yan shi'a a garin Banias a ranakun Juma'a da Asabar.

Masu fafutukar sun ce daruruwan mutane na ta kokarin ficewa daga garin Banias din bayan kisan kiyashin da aka yi kwananan a garin.

Masu fafutukar sun sa wani hotan bidiyo a yanar gizo wanda aka ce yau da safannan ne aka dauka na nuna kisan gillar da aka yi a wuraran, ko dayake BBC ba ta tabbatar da sahihancinsa ba.

Amma dai hotan bidiyan ya nuna yadda aka yiwa wasu mata da yara kanana yankan rago a gidajansu.

Masu fafutuka da 'yan adawa a Syria na zargin gwamnati da kaddamar da wani shiri na kawar da mabiya wasu mazhabobi, a kokarin da ta ke na kafa wata kasa ta mabiya Alawi.

Karin bayani