An hana fita a garin Wukari

Rundunar 'yan sandan jahar Taraba ta ce, ta kama wasu mutane da take zargi da hannu a tashin hankalin da ya auku ranar juma'a, da kuma wayewar garin yau.

Rundunar ta ce ta kama kimanin mutane talatin kuma tana cigaba da gudanar da bincike.

Dazu ne kuma kuma mai rikon mukamin gwamnan jahar, Alhaji Garba Umar ya yi jawabi ga jama'ar jihar, inda ya bayyana rashin jin dadin gwamnati dangane da tashin hankali da ya auku a Wukari.

A jiya ne dai rikicin ya barke tsakanin matasa musulmai da kirista a lokacin da ake bikin binne wani basarake dan kabilar Jukun.

Tuni dai aka saka dokar hana fita ta sa'o'i 24 a garan na Wukari.