Malaysia: Ana ƙidaya ƙuri'u

Bayan al'ummar Malaysia sun kaɗa ƙuri'a a zaɓen da ake gani zai zamo mafi mahimmanci a tarihin a kasar, yanzu haka ci gaba da ƙidaya ƙuri'un.

A karon farko tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai fiye da shekaru hamsin da suka gabata, akwai yiwuwar jam'iyyar hadaka mai mulkin kasar zata iya faduwa a zaben.

Wakilin BBC a babban birnin kasar Kuwala Lampu ya ce, jama'a sun yi dogon layi domin kada kuri'ansu awajen cibiyoyin zabe tun kafin fara kada kuri'ar.

Hadakar jam'iyyar dai na goyon bayan Firaminsta Najib Razak wanda ya ke fuskantar babban kalubale daga jam'iyyun adawa wadda tsohon mataimakin Firaminstan Anwar Ibrahim ke jagoranta.

Mai magana da yawun wata hadakar kungiyoyin da ke sa ido akan zaben, Irene Fernandez ta ce bayanan da aka samu a baya bayan nan su nu na tururwar mutane da ake samu daga Sabah da kuma Sarawak.