Zaman dar-dar tsakanin kasashen Sudan

An harbe fitattacen basaraken kabilar Dinka a Sudan ta kudu a lokacin wani rikici da aka yi tsakanin kabilar laraba ta Misseriya da na Dinka a yankin Abyie.

An harbe fitattacen basaraken ne Kual Deng Majok na kabilar Dinka a lokacin wani rikici da aka yi tsakanin kabilar laraba ta Misseriya da kuma dakarun kiyayen zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.

Rahotanni dai sun ce akwai dakarun majalisar dinkin duniya da suka samu rauni sakamakon artabun da aka yi.

An dai takkadama ne akan yankin Abyei mai arzikin man fetur tsakanin Sudan ta kudu da Sudan.

Rikicin da ya yi ajalin basaraken ya faro ne bayan takkadamar da aka samu game da wasu filaye tsakanin manoma dake goyon bayan kabilar Dinka dake Sudan ta kudu da kuma makiyaya Larabawa daga arewa.

Rahotanni dai sun ce Kabilar Misseriya dai sun tsare wasu jerin gwamnon motocin jami'an Sudan ta kudu ne kuma suna tautaunawa ne game da rikicin sai wani sojan majalisar Dinkin Duniya dake rakiyar motocin ya harbi daya daga cikinsu.

Anan ne kuma suka harzuka inda aka kashe basaraken a artabun da ya biyo baya.

Sudan da Sudan ta kudu dai sun yi fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini wanda aka yi kiyasin cewa ya asarar rayuka miliyan daya da rabi a yankin basasan da kasashen biyu suka yi.