Syria: Ta bada ƙarin haske akan harin Isra'ila

Image caption Wuraren harin Israila ya shafa a Syria

Syria ta bada ƙarin haske game da hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a kasar a ranar Lahadi, lamarin da ya shafi wasu wurare na aikin sojan Syria a birnin Damascus.

Syriar ta ce baya ga Cibiyar bincike ta Jamraya dake kusa da Damascus, jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a kan wasu wurare a kusa da iyaka da Lebanon da kuma wani filin saukar jiragen sama na soja.

Gwamnatin Syriar ta ce an kashe jamaa masu yawa, kuma wasu karin da dama sun samu raunika, amma ba ta fadi adadinsu ba.

Wani shafin Intanat mai goyon bayan 'yan adawa a Syriar, ya ce akalla sojoji araba'in da biyu ne aka kashe a hare-haren da Isra'ila ta kai, kuma wasu karin da dama sun ɓata.