Majalisa ta haramta wa jami’an Gaddafi rike mukamai

Masu goyon bayan dokar haramta wa jami'an Gaddafi rike mukamai
Image caption 'Yan majalisa 164 ne suka kada kuri'ar goyon bayan dokar, yayin da wasu hudu suka nuna adawa, cikin wakilai 200 dake majalisar

Majalisar dokokin Libya ta haramtawa jami’an hambararriyar gwamnatin marigayi Mu’ammar Gaddafi rike mukamai.

Hakan ya biyo bayan amince wa da wata dokar, wacce ta hana tsofaffin jami’an rike mukaman siyasa.

Kada kuri’ar amince wa da dokar ya zo ne, mako guda bayan wasu kungiyoyin mutanen dake dauke da makamai sun yi wa ma’aikatun shari’a da ta harkokin kasashen waje zobe.

Sabuwar dokar dai za ta shafi manyan jami’an gwamnatin Gaddafi, ciki har da Firai minista Ali Zeidan.

Mr. Zeidan da kakakin majalisar dokokin Mohamed Megaryef dukkansu jami’an diplomasiyya ne, kafin juyin-juyi halin da aka yi a kasar.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ce dokar ta zama ta kan mai uwa da wabi, a kan jami’an da suka rike mukamai, a tsawon shekaru arba’in na mulkin marigayi Mu’ammar Gaddafi.