Jirgin sojan Najeriya yayi hatsari

Image caption Akwai dakarun Najeriya a Mali

Wani jirgin sojan saman Najeriya yayi hatsari dazu a ƙauyen Dargol dake da nisan kilomita sittin daga Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar. Matuƙa jirgin biyu sun mutu.

Wata sanarwa daga hedikwatar tsaro ta Najeriya tace, jirgin da yayi hatsarin ɗaya ne daga cikin huɗu irinsa dake aiki a rundunar kasashen yammacin Afurka dake kasar Mali.

Rundunar tsaron Najeriya ta kuma ce, tuni aka soma bincike domin gano musabbabin hatsarin.

Najeriya dai na daga cikin kasashen dake kan gaba wajen tallafawa kokarin fatattakar 'yan tawaye daga arewacin Mali.