Birtaniya: Taron kasa da kasa kan kasar Somalia

Shugaban Somalia Sheik Hassan Mahmud da Fira Ministan Birtaniya David Cameron
Image caption Shugaban Somalia Seik Hassan Mahmud da Fira Ministan Birtaniya David Cameron

A yau ne wakilan kasashe hamsin da wasu kungiyoyin kasa da kasa zasu fara wani taro a Burtaniya domin tattaunawa akan kasar Somalia.

Taron wanda Fira Ministan Birtaniya David Cameron da shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mahmoud zasu jagoranta, zai maida hankali ne akan harkar tsaro da shari'a da kuma batutuwan da suka shafi kula da bangarorin kudaden gwamnati.

Mr Cameron ya bayyana cewa, yana fatan taron zai amince da hanyoyi da zasu samar da tsaro na lokaci mai tsawo a kasar Somalia, tare da samar da shugabanci na gari a kasar.

An dai samu ci gaba a bangaren tsaro a wasu sassa na kasar ta Somalia, sai dai har yanzu 'yan kungiyar Al-Shabaab ne ke rike da iko a wasu sassa da dama na kasar.