An cafke tsohon daraktan hukumar wutar lantarki a Nijar

Tutar jamhuriyyar Nijar
Image caption Tutar jamhuriyyar Nijar

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun cafke tsohon shugaban kamfanin wutar lantari ta kasar Nigelec, bisa zargin sama da fadi da kudi kimanin biliyan 20 na cfa.

Tun bayan kama Malam Fukori Ibrahim wanda kuma dan majalisar dokoki ne, ana cigaba da rufe shi a gidan kason Kolo dake kasar.

Kamun na malam Fukori wani bangare ne na yunkurin da gwamnatin Mahamadou Issoufou, ta sa gaba na yaki da cin hanci da rashawa.

Ko a watan Faburairu ma dai gwamnatin ta kama wasu jami’an ma’aikatar kiwon lafiya sama da 20 bisa zarginsu da almundahana.