Korea ta Arewa ta janye makamai masu linzami

Makamai masu linzami a kasar Korea ta Arewa
Image caption Makamai masu linzami a kasar Korea ta Arewa

Amurka ta ce Korea ta Arewa ta kwashe makamai masu linzami biyu masu cin matsakaicin zango daga wurin kaddamar da su a gabashin tekun kasar.

Wannan mataki ya nuna cewa babu sauran wata barazanar gwajin makaman, kana kuma ya nuna kara rage duk wata damuwa a yankin Korea.

Sai dai kuma Kasar Korea da Arewar, ta yi wani sabon gargadi ga kasashen Korea ta Kudu da Amurka cewa zata maida martanin soji kan duk wani yunkurin keta haddinta.

A watan da ya gabata ta jaddada barazanar kai hari kan kasashen biyu, kana ta dauki wasu matakan da suka haddasa damuwa a yankin Korea.

Kasashen Amurka da kawayenta sun shiga cikin shirin ko ta kwana, kan yiwuwar barazanar gwajin makaman, inda suka kara tsaurara matakan kare kai.

A wani lokaci dai, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya gargadi kasar ta Korea Arewar cewa, kaddamar da gwajin makaman masu linzami babban kuskure ne.

Batun janye makamai masu linzamin daga wurin kaddamar da gwajin nasu, ya nuna cewa hakan zai kawo karshen duk wata barazana.

Amma kuma mahukuntan Amurka na yin gargadin cewa kada a yi saurin murna, idan a ka yi la'akari halayyar kasar Korea ta Arewar na rashin tabbas.