'Akwai bukatar sake gina Somalia'

Taron kasa da kasa a kan Somalia
Image caption Wakilai daga kasashe da kungiyoyi masu bada agaji ne ke halartar taron

Firai ministan Birtaniya David Cameron ya ce yana da matukar muhimmanci a sake gina kasar Somalia, domin kauce wa kaurar dimbin mutane daga can, da kuma yaduwar ayyukan ta'addanci a wasu kasashe.

Mr Cameron ya ce an samu "gagarumin ci gaba" a kokarin da ake yi na kawo karshen yakin da aka shafe shekara da shekaru ana yi a Somalia.

Yana karbar bakuncin taro na musamman ne kan kasar ta Somalia tare da shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud domin taimakawa kasar ta sake gina kanta.

Ana yiwa Somalia kallon wata kasa da ta daidai ce, wacce ke fama da matsalolin 'yan gwagwarmaya, masu fashin jiragen ruwa da matsalar karancin abinci daga shekara ta 2010 zuwa 2012.

Wakilai daga kasashe da kungiyoyi masu bada agaji sama da hamsin ne ke halartar taron na birnin London.

Mr Cameron, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Somaliar na kokarin kwatanta gaskiya da gudanar da al'amurra ba tare da kumbiya-kumbiya ba.

A nasa bangaren Sheikh Mohamud ya ce gwamnati za ta karbi iko da dukkan al'amuran tsaro nan da shekara ta 2015.

Gwamnatin - wacce ta kama aiki bara - ta dogara ne kan dakarun kungiyar Tarayyar Afrika 18,000 da ke kasar.

Kungiyar Al-Shabab, wacce ke da alaka da al-Qaeda, na tayar da kayar baya tun shekara ta 2007, inda a baya ta kwace iko da gwamnati kuma har yanzu tana rike da wasu sassan kasar da dama.

Karin bayani