Ana wani gagarumin taro a kan Somalia

Kasar Somalia ta shafe shekarau sama da ashirin tana fama da tashin hankali
Image caption Kasar Somalia ta shafe sama da shekaru ashirin tana fama da tashin hankali

Wakilai daga kasashe fiye da 50 da kuma kungiyoyi na kasa da kasa sun hallara a London domin fara wani gagarumin taro akan Somalia.

Firayi Ministan Birttania da kuma Shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud ne ke karbar bakuncin taron.

Mr Cameron ya ce yana fatan taron zai kai ga amincewa akan shiri na dogon lokaci domin samun zaman lafiya a Somalia tare da kuma kyautata gudanar da harkokin mulki ba tare da kumbiya-kumbiya ba.

Yanayin tsaro ya inganta a cikin kasar ta Somalia, to amma har yanzu, sassa da dama na kasar suna karkashin ikon kungiyar masu kishin Islama ta Al-Shabaab, inda ikon gwamnatin kasar ya takaita kusan ga Mogadishu, babban birnin kasar kawai.