Brahimi yayi marhabin da yunkurin ceto Syria

Lakhdar Brahimi
Image caption Lakhdar Brahimi

Mai shiga tsakani a Syria na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa , Lakhdar Brahimi ya yi marhabin da aniyar da Rasha da Amurka suka nuna na yin aiki tare domin kawo karshen rikicin Syriar.

Lakhdar Brahimi ya ce shi ne labari mai karfafa gwiwa a kan Syria da ya fito cikin lokaci mai tsawo, -- to amma yayi gargadin cewar wannan matakin farko ne kawai.

Lakhdar Brahimi ya shaidawa BBC cewar yana fatan sanarwar da ta fito daga hukumomin Rasha zata kasance wani abinda zai zaburar da dukkan wadanda lamarin ya shafa. Kuma za su yi tunanin al'umar Syria ne kawai da yadda za a iya ceto kasar.

Ranar Talata Amurka da Rasha sun bayyana shirin gudanar da wani taron kasa da kasa a kan Syriar , sannan suka amince su karfafa wa gwamnatin Syriar da kungiyoyin 'yan adawa su sasanta, sakamakon wata tattaunawa a Moscow.