Afrika na tafka asara - Annan

Kofi Annan
Image caption Kofi Annan ya ce akwai bukatar sauya yadda ake mulki

Wani kwamiti da tsohon Sakatare Janar na MDD Kofi Annan ke jagoranta, ya yi gargadin cewa kaucewa biyan haraji, da cinikin bayan fage da musayar kudade ta hanyoyin da basu dace ba, na hana kasashen Afrika amfana daga dimbin albarkatun da Allah ya hore musu.

Mr Annan wanda ke shuagabantar kwamitin kula da ci gaban Afrika, ya shaida wa BBC cewa wannan kamar kwace abinci ne daga bakin talaka.

Rahoton ya ce yadda kamfanoni ke mayar da ribar da suke samu zuwa kasashen da ba a biyan haraji sosai, yana sa Afrika asarar dala biliyan 34 a kowacce shekara.

Abinda Mr Annan ya ce ba karamar illa yake yi ga rayuwar jama'a a nahiyarba musamman talakawa:

"Harta kasashen da suka ci gaba sunga illar da rashin biyan haraji yake haifarwa, a don haka Turai da Amurka suke bullo da dokokin da za su kare su.

Ana su bangaren idan kamfanin ya ki biyan haraji ko kuma ya mayar da kudade zuwa kasashen waje, abinda za su rasa haraji ne kawai.

Amma a nahiyarmu ta Afrika, wannan na shafar mata da kananan yara, a wasu lokutan kamar ka kwashe abinci ne daga bakin talaka," in ji Mr Annan.

Kofi Annan ya ce kasashen Afrika na bukatar kyautata yadda suke gudanar da mulki, kuma ya kamata kasashe mafiya arziki a duniya su bullo da dokoki na tabbatar da gaskiya da biyan haraji.

"Ba ma samun abinda ya kamata mu samu daga albarkatun kasashenmu. Ba ma samun kudaden shigar da ya kamata, saboda cin hanci da rashawa," a cewarsa.

Karin bayani