Isra'ila ta amince a gina gidaje 300

Gwamnatin Isra'ila ta bada ikon gina kimanin gidaje ɗari uku a wani wuri dake kusa da gaɓar yammacin kogin Jordan, a garin Ramallah.

Sai dai kuma ƙungiyoyin fafutukar samar da zaman lafiya na Isra'ila sun soki wannan matakin.

An ambato wani babban jami'in Palesɗinu, Saeb Erakat yana yin tir da matakin, yana mai cewa yunkuri ne da Isra'ila ke yi na yin zagon ƙasa ga ƙoƙarin da sakataran harkokin wajan Amurka John Kerry ke yi na a sake komawa tattaunawar zaman lafiya.

Batun gina sabbin matsugunnen Yahuda dai na daga cikin abubuwan dake yin karan tsaye ga ƙoƙarin komawa kan teburin sulhu tsakanin Isra'ila da Palasɗinawa.