'Yan sanda 47 aka kashe a harin Nassarawa

Goodluck Jonathan
Image caption An kashe akalla 'yan sanda 30 a jihar Nassarawa yayin da wasu 17 suka yi batan dabo

Rundunar 'yan sanda a jihar Nasarawa ta ce jami'anta arba'in da bakwai ne aka kashe a wani harin kwantan bauna da ake zargin wasu 'yan kungiyar matsafa ta Ombatse ta kabilar Eggon suka yi a kauyen Lakyion dake karamar hukumar Lafiya a jihar.

Rundunar 'yan sandan ta kuma ce jami'anta ashirin da takwas ne suka tsira a harin.

Yanzu haka wasu rahotanni daga garin Akwanga na jihar Nasarawar na cewa matan 'yan sanda da aka kashe mazajensu, sun toshe babbar hanyar Akwanga zuwa lafiya babban birnin jihar, kuma sun ce ba za su bude ba har sai an ba su gawrawakin mazajensu

A halin da ake ciki kuma Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan yana ganawa da shugabannin rundunonin tsaro na kasa kan matsalolin tsaron da kuma tashe tashen hankulan da Najeriyar ta fuska a cikin yan kwanakin nan.

Tun farko dai Shugaban ya katse ziyarar da ya kai kasar Afrika ta Kudu domin fuskantar tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a kasar a baya-bayan nan.

Wata sanarwa daga ofishin shugaban ta ce, ya kuma fasa kai ziyara kasar Namibia kamar yadda aka tsara tun farko.

Ta kara da cewa shugaban ya dawo kasar ne domin ya jagoranci yunkurin da jami'an tsaro suke yi na shawo kan tashin hankalin da aka fuskanta a wannan makon a jihohin Borno, Plateau da Nassarawa.

An kama dan sanda

Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce an kama wani dan sanda wanda ake zargin dan kungiyar nan ce ta Ombatse bisa zargin taimakawa 'ya'yan kungiyar da labaran sirri na 'yan sanda.

Dan sandan na daga cikin wadanda aka tura su garin Alakyo domin kama Baba Alakyo matsafin nan da ake zargin yana bawa 'ya'yan kungiyar ta Ombatse asirin bindiga.

Motar dan sandan ce kawai ba a kona ba a kwantan bauna da 'ya'yan kungiyar suka yi wa 'yan sanda, abinda ya yi sanadiyar kisan da dama daga cikinsu.

Bayanai sun kuma nuna cewa an gano bindigogin 'yan sanda a gidan sa.

A kalla 'yan sanda 30 ne ake zargin 'yan kungiyar matsafan ta Ombatse suka kashe a kauyen Alakyo na jihar Nassarawa, yayin da wasu 17 suka bata.

Can a garin Bama ma an kashe mutane 55 yawancinsu jami'an tsaro a wani hari da ake zargin 'ya'yan kungiyar Boko Haram da kaiwa.

Ganawa da 'yan Boko Haram

Najeriya na fama da hare-haren da ake dangantawa da kungiyar da ake kira Boko Haram - wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane daga shekara ta 2009.

A wata hira da BBC, tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar, ya dora alhakin tabarbarewar tsaron da gwamnatin kasar, yana mai cewa ba a baiwa jami'an tsaro kayan aikin da ya kamata.

Sai dai ana ta bangaren, gwamnati na ci gaba da yunkurin da ta ce tana yi na shawo kan matsalar.

Ko a ranar Alhamis kwamitin da gwamnati ta kafa domin tattaunawa da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram ya gana da wasu 'ya'yan kungiyar da ake tsare da su a gidan yari na Kuje da ke Abuja.

Shugaban kwamitin kuma ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu, ya shaida wa Naziru Mikailu cewa sun je gidan yarin na Kuje ne domin samun bayanan da za su kai ga ganawa da shugabannin kungiyar.

Karin bayani