An ceto wata mata da rai a Bangladesh

Matar da aka ceto a Bangladesh
Image caption Matar da aka ceto a Bangladesh

An ceto wata mata da ranta daga cikin buraguzan ginin masana'antar da ya rushe a Bangladesh kwana 17 tun bayan bala'in.

Hakan ya faru ne yayinda adadin mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar rugujewar ginin ya haura dubu daya.

Tawagogin ceto na bayyana lamarin a matsayin wani abun al'ajabi.

Sun sallamar da cewar za su samu wani da ransa.To amma yayinda sojoji suke kwashe tarkace sun ji wani kara a karkashi.

An kai na'urar ceto a wurin inda aka ga wata mata tana daga hannu.

Ta yi kururuwar cewar har yanzu ina nan, kuma ta ce sunanta Reshma.

An shiga cikin 'yar damuwa yayinda sojoji da yan kwana kwana suka kai na'urar yanka karafa domin samu a fitar da ita daga cikin buraguzan.

A halin yanzu dai an kai ta asubiti.