An rufe babban asibitin Maiduguri

Maiduguri
Image caption Harin da aka kai a Bama ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 55

Likitoci sun rufe babban asibitin birnin Maiduguri na Arewa maso gabashin Najeriya bisa zargin cin zarafin ma'aikata da marasa lafiya da 'yan sanda suka yi.

Sun ce jami'an tsaron sun yi fushi ne saboda dakin ajiye gawarwaki na asibitin ya cika ta yadda ba za a iya ajiye gawarwakin 'yan sandan da 'yan bindiga suka kashe ba.

Daya daga cikin likitocin ya shaida wa BBC cewa ba za su sake karbar marasa lafiya ba har sai gwamnati ta samar musu da cikakken tsaro domin su gudanar da ayyukansu.

Har yanzu 'yan sanda basu ce komai game da lamarin ba.

'An karya likita daya'

Birnin Maiduguri ya dade yana fama da hare-haren kungiyar Boko Haram tun daga shekara ta 2009.

Mutane hamsin da biyar aka kashe a wani hari da 'yan bindiga suka kai ranar Talata a garin Bama mai nisan kilo mita 70 daga Maiduguri.

An kona ofishin 'yan sanda da barikin soji da sauran gine-ginen gwamnati a lokacin harin.

A ranar Alhamis ne aka kai wasu gawarwaki asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri, sai dai ma'aikatan asibitin sun ce hayaniya ta barke lokacin da aka cewa 'yan sanda wurin ajiye gawarwakin ya cika.

Shugaban kungiyar likitoci na cikin gida Dr Yahaya Muhammed, ya ce an karya wani likita daya a kafa sannan aka mari wani.

Karin bayani