An fara kada kuri'a a zaben Pakistan

An fara kada kuri'a a zaben Pakistan
Image caption An bada rahotannin samun dogayen layuka a sassan kasar da dama

Miliyoyin 'yan kasar Pakistan sun fara kada kuri'a a zaben kasar na gama-gari. Wannan ne karon farko da za a samu musayar mulki tsakanin gwamnatocin farar hula.

Sai dai wani bam da ya tashi jim kadan bayan fara zabe a birnin Karachi ya kashe mutane da dama.

Rahotanni sun nuna cewa an fara samun dogayen layuka a runfunan kada kuri'a a sassa daban-daban na kasar - cikin masu kada kuri'ar har da mata.

Wannan shi ne zabe mafi muhimmanci a tarihin Pakistan, domin a karon farko, za a samu musayar mulki tsakanin gwamnatocin farar hula a tarihin kasar na shekaru 66 da kafawa.

Masu kada kuri'a za su zabi 'yan majalisar dokoki da majalisun lardi guda hudu, wadanda za su zabi sabon Fira minista da kuma shugabannin larduna.

Masu sharhi na ganin za a yi kan-kan-kan tsakanin 'yan takarar - na gaba-gaba sun ne tsohon Fira ministan Nawaz Sharif da fitaccen dan wasan Kuriket Imran Khan.

Sai dai tashe-tashen hankula ba kakkautawa sun mamaye yakin neman zaben, sannan kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Taliban ta sha alwashin kaddamar da hare-hare a ranar zaben.

Amma gwamnati na kokarin tabbatar da tsaron lafiyar jama'a, inda za a samar da fiye da jami'an tsaro dubu dari shida (600,000) da suka hada da sojoji dubu hamsin (50,000), domin hana 'yan gwagwarmaya kai hare-hare.

An ci gaba da fuskantar tashin hankali har zuwa ranar karshe ta yakin neman zabe, inda aka kama dan tsohon Fira minista Yousuf Raza Gilani.

Karin bayani