Tunawa da wadanda suka mutu a Beichuan

Tunawa da wadanda suka mutu a Beichuan
Image caption Kimanin mutane 90,000 ne suka rasa rayukansu

Kasar China na bikin cika shekaru biyar da faruwar daya daga cikin girgizar kasa mafi muni da aka taba yi a kasar.

Kimanin mutane 90,000 ne suka mutu, ciki har da yara 5,000, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a gundumar Sichuan da ke Kudu maso Yammacin kasar.

Daruruwa masu jimami ne suka taru a dan abinda ya rage a yankin Beichuan domin kunna kyandira da kawar da damuwa a wani bangare na nuna jimami ga wadanda suka rasa rayukansu.

Mutane 8605 ne suka rasa rayukansu a kauyen Beichuan kawai - fiye da kashi daya bisa uku na yawan jama'ar garin.

An tattara dan abinda ya rage domin tunawa da girgizar kasar; har yanzu hanyar garin bata koma daidaiba yayin da hasumiyar dogayen gine-gine ke zube saboda buraguzan gini.

A shekaru biyar da suka gabata, an kaddamar da ayyukan sake gine yankuna da dama a gundumar ta Sichuan - abinda ya sa aka samu damar sake tsugunar da mutanen da suka tsira daga bala'in girgizar kasar.

Sai dai har yanzu akwai sauran tambayoyi da ba a amsa ba, game da rawar da sakacin jami'an gwamnati da kuma cin hanci ya taka, wurin rushewar makarantu da dama.

Lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar yara 5000, da kuma kin bayyana dukkan sunayen yaran.

Karin bayani