Kokarin kafa babbar jam'iyyar adawa

Yunkurin kafa jam'iyyar APC
Image caption Jam'iyyun sun sha alwashin kifar da gwamnatin PDP a zaben 2015

A Najeriya jam'iyyar CPC ta yi babban taronta don neman amincewar magoya bayanta game da aniyarta ta dunkulewa da wasu jam'iyyu wajen kafa sabuwar jam'iyyar adawa ta APC.

Dubban magoya bayan jam'iyyar ne suka yi dandazo a Abuja, har ma da shugabannin wasu jam'iyyun adawar kasar, wato A C N da ANPP.

Ita ma dai jam'iyyar ANPP a yau ta yi nata babban taron a Gusau, babban birnin jahar Zamfara, inda kusoshinta daga duk fadin kasar suka halarta.

A wajan taron na ANPP din kuma jam'iyyar ta amince da hadewa da wasu jam'iyyun adawa dan kafa jam'iyyar APC da ake saran ta zama babbar jam'iyyar adawa wadda zata tunkari jam'iyyar PDP a zaben shekara ta 2015.