Pakistan: Nawaz Sharif na 'gab da nasara'

Pakistan
Image caption An samu fitowar jama'a da ba a taba samun irinta ba

Tsohon Fira Ministan Pakistan Nawaz Sharif na bikin murna tare da magoya bayansa bayan da alamun farko na sakamakon zaben kasar ya nuna cewa jam'iyyarsa ce za ta zamo kan gaba a Majalisar dokoki.

Kiyasin kafafen yada labarai game da sakamakon zaben da aka samu kawo yanzu, ya nuna cewa jam'iyyarsa ta Muslim League na kan gaba, kuma tuni ya yi ikirarin samun nasara.

Wannan zaben ne zai haifar da musayar mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata a karon farko a tarihin kasar.

Jama'a da dama ne suka fito domin kada kuri'unsu sai dai an samu tashe-tashen hankula.

A birnin Karachi, kungiyar Taliban ta dauki alhakin bam din da ya tashi wanda ya kashe mutane 11 sannan ya jikkata wasu 40.

An dasa bam din ne a wajen ofishin jam'iyyar Awami National Party.

'Mu godewa Allah'

Hakazalika an samu wasu karin hare-haren a yankin Balochistan da kuma birnin Peshawar da ke Arewa maso Yammacin kasar.

An kara lokacin kada kuri'a da tsawon sa'a daya a dukkan fadin kasar kafin a rufe rumfunan zabe da misalin karfe 6.00 na yamma wato karfe (daya agogon GMT).

Babu sakamako a hukumance kawo yanzu, amma sakamakon farko-farko ya nuna cewa jam'iyyar Mr Sharif na kan gaba a mazabu kusan fiye da 100 cikin 272 da aka gudanar da zaben 'yan majalisu kai tsaye.

Sai dai babu tabbas kan ko za su iya samun rinjaye kai tsaye a majalisar dokokin.

Da yake magana a gaban magoya bayansa a birnin Lahore, Mr Sharif ya ce ba makawa Muslim League (PML-N) ce za ta zamo babbar jam'iyya.

"Ya kamata mu godewa Allah da ya baiwa Muslim League (PML-N) damar sake shugabantarku da kuma Pakistan."

Sai dai wakilin BBC a birnin Owen Bennett Jones, ya ce yanayin da magoya bayansa ke ciki ba na murna bane, ganin cewa akwai babban kalubale da ke fuskantar kasar.

Karin bayani