An kona barikin 'yan sanda a Bama

Rahotanni daga garin Bama a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya na cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani barikin 'yan sanda da ke bayan garin, inda suka cinna masa wuta a tsakar daren jiya, lamarin da ya haifar da asarar kaya na miliyoyin nairori.

Mazauna garin sun ce wasu mutane ne suka zo inda suka kori dukkan mutanan dake cikin barikin 'yan sandan kafin su cinna masa wuta.

Kawo yanzu jami'an 'yan sandan basu ce komai ba game da lamarin.

A wani labarin kuma an yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da wasu 'yan bindiga a garin Jambutu dake wajan birnin Yola a tsakaddaran jiya, inda aka kashe mutane shida.

Jami'an 'yan sandan jahar Adamawa sun tabbatar da afkuwar lamarin, sun kuma ce an kama 'yan bindigar da dama.