David Cameron na ziyara a Amurka

David Cameron
Image caption David Cameron na fuskantar kalubale kan Tarayyar Turai

Fira Ministan Burtaniya David Cameron na birnin Washington domin tattauna yadda za a kulla yarjejeniyar kasuwanci da ba shamaki tsakanin Amurka da na hiyar Turai a daidai lokacin da ake ci gaba da tattauna makomar kasar a Turan.

A ranar Lahadi wasu Ministoci sun fada a bayyane cewa za su goya wa Burtaniya baya ta fice daga Tarayyar Turai idan da za a kada kuri'ar raba-gardama a yanzu.

Sai dai magajin garin London Boris Johnson ya ce koma bayan da kasar ke fuskanta na faruwa ne saboda lalaci da rashin yin katabus, dan haka, ba za su magance matsalar ba ta hanyar fita daga Tarayyar ta Turai.

Bambancin dai a zahiri ya ke. A gida ministoci kamar su Michael Gove da Philip Hammond suna magana a kan ficewa daga Tarayyar turai.

Batun Syria ma...

Sai dai a Amurka, David Cameron yana magana ne kan irin muhimmancin da tarayyar Turai ke da shi.

Fira minista Cameron zai je fadar White House domin ganin an samar da sabuwar jarjejeniyar kasuwanci tsakanin Amurka da Turan - yarjejeniya mara shamaki, wacce ya ce za ta samar da fan biliyan goma ga tattalin arzikin Burtaniya a kowacce shekara.

Mr Cameron ya bayyana ta da cewa abu ne da ke faruwa sau daya a kowanne zamani, sannan ya ce yana fatan fara tattaunawa a hukumance da shugaba Obama, a taron kungiyar kasashe 8 masu arzikin masana'antu da za a yi a watan gobe.

Sai dai wannan tattaunawa ka iya daukar shekaru - shekarun da har sai fa Burtaniya ta ci gaba da kasancewa a Tarayyar Turai, abinda Amurka ta ce tana son ganin ya faru, amma kuma da dama daga cikin 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar Mr Cameron ba sa so.

David Cameron da shugaba Obama za kuma su tattauna akan rikicin Syria.

Karin bayani