Nawaz Sharif na kokarin kafa gwamnati

Nawaz Sharif
Image caption Nawaz Sharif an duba yiwuwar samun rinjaye a Majalisa

Jagoran jam'iyyar Muslim League a Pakistan, Nawaz Sharif, ya tattauna da shugabannin sauran jam'iyyu kan kafa wata sabuwar gwamnati, bayan zaban da akai jiya a kasar.

Sakamakon zaben da ba na hukuma ba na nuna cewa jam'iyyar Muslim League za ta yi nasara da gagarumin rinjaye.

ko dayake za ta nemi goyan bayan sauran jam'iyyu domin kafa gwamnati.

Tuni Nawaz Sharif ya fara kai kawon hada gwamnatin da zai jagoranta a matsayin Praminista kawo na 3, bayan wani juyin mulki da ya kawo karshen mulkinsa shakaru 14n da suka wuce.

Jama'a da dama dai a Pakistan na bayyana fatansu game da sabuwar gwamnatin da jam'iyyar Nawaz Sahrif z ata kafa.

Tuni dai tsohon dan wasan kurket wanda zai zama babban abokin hammaya a kasar, wato Imran Khan ya taya jama'ar Pakistan murna da fitowar da sukai kwasu da kwarkwata suka kada kuri'a, amma ya ce batun magudin zaben da ake ce anyi ba abu ne mai dadin ji ba.

A lokacin yakin neman zabe, Nawaz Sahrif ya yi alkawarin kafa kakkarfar gwamnati---- Kuma masu kada kuri'a sun nuna cewa zasu tabbatar da 'yan siyasa sun yi aikin da ya kamata a wannan karon fiye da baya.

Karin bayani