Syria ta musanta hannu a harin Turkiyya

Racep Tayyip Erdogan
Image caption Racep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya za ta yi aiki da hankali

Kasar Syria ta musanta hannu a harin bama-baman da suka kashe mutane 46 a garin Reyhanli na kasar Turkiyya ranar Asabar.

Fira Ministan Turkiyya, Racep Tayyip Erdogan, ya ce munanan hare-haren bama-bamai a mota guda biyu, da aka yi a garin Reyhanli na kan iyaka a Turkiyyar, nufinsa shi ne a ingiza kasar ta yi yaki da Syria.

Ya shaida wa magoya bayansa cewa lalle ne Turkiyyar ta yi aiki da hankali a lokacin da ake takalarta.

Ministan watsa labarai Imran al Zoubi, ya ce kusan a Turkiyyar ce ke da alhakin haka bisa jawo ma kanta da ta yi.

Ya ce: "Mu abin da muke cewa shi ne, duk wani abu da ya auku a Syria alhakin gwamnatin Turkiyya ne da sauran ire-irenta, shakka babu."

Mutane arba’in ne suka rasa rayukansu a wadannan hare-hare, yayin da fiye da mutane dari suka sami raunuka.