Turkiyya ta yi gargadi kan harin bam

Harin bama bamai a Turkiyya
Image caption Harin bama-bamai ya yi barna matuka

Kasar Turkiyya ta yi gargadin cewa za ta dauki duk wani mataki da ya kamata dan kare kanta, bayan da wasu bama-bamai suka tashi a cikin wasu motoci a wani gari da ke iyakar kasar da Syria.

Akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu a garin Reyhanli, inda da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar Syria ke fakewa.

Gwamnatin Turkiyya ta ce ta na zargin wata kungiya da ke da alaka da hukumar leken asiri ta Syria da kai harin.

Kasar Turkiyya dai na daga cikin manyan magoya bayan 'yan adawa da ke yakar gwamnatin kasar Syria.

Mutane fiye da dari ne suka sami raunuka a fashewar a garin Reyhanli, inda ke da 'yan gudun hijirar yakin da ake yi a Syria.

Wani da ya ga abin da ya faru ya ce "Bom din ya fashe ne ba zato ba tsammani. Ina tsaye ne a can sai kawai bam din ya tashi."

Mataimakin Fira ministan Turkiyya ya ce sojin leken asiri na Syria ne ake zargi da kai harin.